Bidiyo: Magidanci 'Dan Najerya ya Gwangwaje Matarsa da Kyautar Adaidaita Sahu 2 Ranar Bazday Dinta

Wani bidiyo da @nesta_surprise8 ta wallafa ya nuna lokacin da mata ta kasa daina kukan farin cikin yadda mijinta ya yi amfani da N500,000 don gina ma ta ginin kudi .

Ya bata kyautar adaidaita 2 don sana'a Don tabbatar da matar ta samu wata hanyar samun sulalla, mutumin ya siyo ma ta sabbin adaidaita sahu biyu. Ya kara ma ta da waya kirar Iphone 14 da agogon Lu'u-lu'u don ya dace da kyautar.

Matar ta dauki hotuna da sabbin adaidaita sahu biyu, inda mutane da dama a shafin tsokacin wallafar suka lakabawa mijin sunan mijin da yafi kowanne nuna kauna a shekarar. Daga lokacin da aka tattara wannan rahoton, bidiyon ya janyo sama da tsokaci 2,000 da sama da jinjina 90,000 

News source@ Legit hausa

Post a Comment

Previous Post Next Post